14 Oktoba 2016 - 10:50
Afirka Ta Tsakiya: An Kashe Mutane 20 A sabon Rikicin Kasar

Mutane 20 Sun Mutu A Rikicin Kasar Afirka ta Tsakiya

Dakarun Tabbatar da zaman lafiya a kasar Afirka ta tsakiya sun sanar da mutuwar mutane 20 a sabon rikicin da ya barke a kasar.

Kamfanin Dillancin labarun Associated Press daga birnin Bongui ya ambato kwamandan dakarun tabbatar da zaman lafiya, Renar Onana yana cewa; A yankin Kaga-Bandoro an kashe mutane 20 da kuma jikkata wasu 41.

Kwamandan dakarun tabbatar da zaman lafiyar  ya kara da cewa; Rikicin wanda ya barke a jiya alhamis ya faru ne a kusa da sansanin dakarun tabbatar da zaman lafiyar.

Duk da cewa an sami koma bayan tashe-tashen hankula a kasar sai dai jefi-jefi ana samun rikici.288